A Lissafi na daga ranar Larba 23rd August 2023 zuwa 1st December 2023 Maigirma Kwamishina Dutsinmari ya cika Kwana 100 a Office amatsayin Kwamishina inda cikin iyawar Allah mutane 7 suka Amfana dashi ta fuskar Samun Motoci domin Su Hau ko suyi Kasuwanci su Dogara da kansu su taimake iyalin su da Sauran Yan'uwan su anawa Lissafi.
KAURAN GWANDU NEW MEDIA INITIATIVE.
MOTTO:- PROMOTING APC AND GOOD GOVERNANCE.
Acikin Kokarin mu na ganin mun Qara daga Darajar APC da kuma Daga Darajar Masu Mulki Kyakkyawa a Jahar Kebbi.
A yau akalar mu zata waiwayi Daya daga cikin Kwamishinonin Jahar Kebbi 26 daga Lokacin da aka Rantsar dasu sunka shiga office sunka kama aiki.
Sanin kowane Shekaranjiya A wajen Bukin Raba motoci ga Kwamishinonin Jahar Kebbi Maigirma Gwamnan Jihar Kebbi H.E Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu yayi kira garesu ga Abubuwa biyu masu muhimmanci acikin Al'umma:-
1. Cewa Su koma cikin Al'ummar su sujiyo Bukatun su sukawo domin Gwannati ta taimake su.
2. Su Taimake Al'ummar su da Abinda sunka samu Gwabnatance.
Sanin kowane tun Ranar da Maigirma Gwamna ya rantsar dasu yafara fadin Wannan Maganar yanzu gashi ya sake fadi a Karo na biyu.
Wannan yassa na dau Alkawalin zanyi Tambihi akan Cikar Kwana 100 ga Hon Commissioner Ministry For Local Government and Chiefftaincy affair Kebbi State Hon Abubakar Umar Garba Abubakar Dutsinmari Sardaunan Bagudo, Majen Gwandu, Ardon Kabi, Kaigaman Yauri, Santurakin Koko, bisa kokarin sa na ganin yayi aiki da Umurnin Maigirma Gwamna H.E Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu.
A Lissafi na daga ranar Larba 23rd August 2023 zuwa 1st December 2023 Maigirma Kwamishina Dutsinmari ya cika Kwana 100 a Office amatsayin Kwamishina inda cikin iyawar Allah mutane 7 suka Amfana dashi ta fuskar Samun Motoci domin Su Hau ko suyi Kasuwanci su Dogara da kansu su taimake iyalin su da Sauran Yan'uwan su anawa Lissafi.
Hotuna da sunayen su na Qasa.
Kuma yakan yiyu basu kadai ne ba domin wasu ana basuwa boye bamu sani domin Sirrinta abubuwan shi wani lokaci.
Shi batun Kyautar Kuddi da Daidaikun Al'umma, Kungiyoyi, Allah yasani ba'a iya lissafa wannan saidai abishi da Addu'a.
Nidai Bance wani ba a iya Sanina daga 1999 zuwa 2023 Anyi Gwamnatoti a baya Guda Ukku 3 wannan itace ta Hudu 4 bansan wani Kwamishina da ankayi mai Kyautatama Al'umma Tamkar Shi ba.
A siyasa yau muna cikin Qarnin da ake cema SIYASA DAIDAI DA ZAMANI watau Mu'amala da "Yan Social Media masu Faɗin Akkhairin "yan Siyasa da kuma Kokarin kare martabar su ga "Yan Adawa.
Kaf Kwamishinonin Jahar Kebbi 26 Hon Garba Dutsinmari ne kaɗai a Jahar Kebbi yake da Matasa "Yan Social Media Kungiyance a Jahar Kebbi a kowace Karamar Hukumar Jahar Kebbi akwai Hoto a Qasa. Acikin wadannan "yan Social Media nashi wasu Lokutta yana kiransu da Yarana kalmar da nikejin Dadi Babba yakira mai yi masa Hidima da ita Musamman in Babban Nan yazan mai taimakon su.
Daga Lokacin da suka Fara yi masa Hidima Siyasance Su wadannan Matasa kashi 70 cikin 100 sun Amfana da wannan Shugaba nasu Alhamdulillahi. Wasu sun Samu Mota, Wasu anbasu Aiki, wasu anbasu Mashin, Wasu anbasu Jari, wasu anbasu gudunmuwa sunyi aure dadai Sauran su.
Shawara ta Zuwa ga MAIGIDA ANAN itace kamar Yadda Maigirma Kwamishina yafadi a ranar da Ya shiga Office cewa yayi aiki a Kananan Hukumomin 18/19 a Jahar Kebbi Alhamdulillahi. Yanzu ga Dama ta samu ta aiki a Kananan Hukumomin 21 dake Jahar Kebbi.
Wata Rana kafada muna Cewa kai ba Wakilin Karamar Hukumar mulki daya ko biyune ba kai na ƙananan Hukumomin Jahar Kebbi ne baki daya. A wannan gaba yakai Maigirma Kwamishina nikeson Bada Shawarar ka bude hannun ka yaqara isa kowace karamar Hukuma domin in munzo magana zamu ce babu ƙaramar hukumar da bakada Wakili watau wanda kabaiwa mota ko mashin ko keke napep a jahar Kebbi.
Yin haka zai qara tabbatar muna da Mafarkin mu nan gaba in Shaa Allahu na ganin Jahar Kebbi ta qara cimma burinta na samun Ingantaccen Jagora in Shaa Allahu.
Haka kuma yadda kake Kyautar Motoci Yakamata ace Shugabannin Kananan Hukumomin ka suma sunayi Gwargwado kamar yadda na Argungu Hon Salihu Ahmad keyi, da Bala Gagga na Yauri da kuma Hon Zayyanu na Maiyama. Wasu daga cikin Chairmomin ka suna bada Kyautar mashuna kamar yadda Hon Shamsu Kalgo keyi da Hon Atiku Kalcha na Gwandu. Yin haka baqaramin inganta Siyasa bane.
Haka Yakamata ace Ma'azanyen kananan hukumomin ka da Sakatarorin ka da mataimakan Shugabannin Kananan Hukumomin nayi wajen bada Kyautukkan Mashuna ko Keke Hawa ga Marayu a Jahar Kebbi idan aka samu haka Shakka Babu a shekaru Biyu masu Zuwa zakaji Akkhairin wannan Gwannati ya yawaita acikin Al'umma.
Zan tsaya anan sai A Kashi na Biyu in Shaa Allahu.
Naka
Hon Yahuza Zaki Gwandu
(Na Gwandu Mai Tambihi)
Jummuat 15th December 2023.
Comments
Post a Comment